Afghanistan na son lura da sha'anin tsaronta-In ji Karzai

Tambarin dake nuni da taro kan tsaron Afghanistan
Image caption Afghanistan na son lura da al'amuran tsaron kanta

An kammala taron kasa da kasa a Afghanistan bayan amincewar da taron yayi da bukatar bayar da karin kusan kashi hamsin cikin dari na kudaden agaji kai tsaye ga gwamnatin kasar.

A halin yanzu dai gwamnatin na karbar kashi ashirin cikin dari ne na kudaden, kuma shugaban kasar Hamid karzai yayi ta kamun kafa don ganin an kara kason.

Shugaban na Afghanistan, ya sake jaddada bukatarsa ta cewar kasar na son daukar alhakin samar da tsaron kanta nan da shekarar 2014.

Ya ce Afghanistan da kasashen yammacin duniya na fuskanta abokin gaba daya ne, wanda ke neman raba hadin kan kasashen.

A wajen taron sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton ta bayyana cewar ana ci gaba da kai kayyayakin aiki da ma'aikata Afghanistan, da suka hada da wasu sabbin dakaru dubu goma na rundunar kawancen kasa da kasa ta ISAF.

A nasa bangaren, babban sakataren Majalisar dinkin duniya Ban Ki-Moon ya ce a baya kasashen duniya daban- daban sun yi kokarin samar da zaman lafiya ba tare da sanya jama'ar kasar a tsare-tsarensu ba.

Afghanistan dai ta karbi tallafin dala biliyan 36 tun daga shekarar 2001,sai dai ba su yi wani tasirin a zo a gani a kasar ba.

An kashe akasarin tallafin wajen tabbatar da tsaron kasar.

Wakilai daga kimanin kasashe saba'in ne ke halartar taron.