Yiwuwar samun man fetur a Nijar

Ana shirye-shiryen fara aikin hakar man fetur a Nijar

Alamu sun nuna cewa Jamhuriyar Nijar nada albarkatun man fetur a wasu yankunan kasar da ke makwaftaka da kasar Chadi.

Hakan ne ya sa a watan Junin shekara ta 2008, kasar China ta kuduri aniyar zuba jarin dala biliyan biyar domin bunkasa harkar neman mai a kasar.

Da farko an saran babban kamfanin man kasar China National Petroleum Corporation (CNPC), zai fara samar da gangar mai a shekara ta 2009, sai dai hakan bai yiwu ba.

Amma ana ci gaba da aiki a yanzu haka, kuma mahukunta sun ce komai na tafiya ba tare da wata matsala ba.

A karkashin wannan yarjejeniya dai, kamfanin CNPC zai gina bututun mai mai nisan kilomita 2000, da kuma matatar mai wacce za ta samar da ganga 20,000 a kowacce rana.

Wannan yunkurin da China ta yi na zuba jari a yankin Agadem da ke makwaftaka da Chadi, shi ne na baya-bayan nan da kasar ke yi domin neman makamashi a Afrika.

Image caption An samu man ne a yankin Agadez mai makwaftaka da kasar Chadi

'Ban gishiri in baka manda'

Ministan kula da harkokin ma'adanai da makamashi na kasar a wancan lokaci Mohammad Abdoulahi, ya bayyana yarjejeniyar da cewa za ta amfani duka bangarorin biyu.

Nijar dai na daya daga cikin kasashen da ke fama da talauci, kuma Majalisar Dinkin Duniya ta sanya ta a mataki na biyar daga kasa a rukunin kasashen da ke da karancin ci gaba.

Kasar ta dade tana fama da matsalar fari da karancin abinci, wanda hakan ya jefa miliyoyin mutane cikin yunwa a shekara ta 2005 da kuma 2010.

Fata na gari

Yankin Gabashin Nijar inda ke da arzikin mai, ba ya cikin yankunan da suka fuskanci tashin hankali a lokacin boren da Abzinawa suka yi.

Amma kasashen duniya ciki har da China sun nemi a kwantar da hankali, domin kasar ta samu ci gaba mai dorewa.

Jama'ar kasar da dama na fatan samun albarkatun man da ka iya bunkasa tattalin arzikin kasar, wanda kuma ka iya taimakawa wajen fitar da su daga kangin talaucin da ya yi musu katutu.