An dade ana cece kuce kan bauta a Nijar

Bauta a Nijar
Image caption Asibit wata baiwa ce data tsere daga wurin mai gidanta

Bautar da jamaa dai matsala ce da aka dade ana fama da ita a duniya. Duk da cewa a hukumance an haramta bauta a wasu kasashen tun kimanin karni biyu da suka gabata, safarar mutane da sanya yara cikin ayyukan wahala har yanzu na nan.

Akwai kasashe da dama a duniya da jama'a kalilan ne kawai ke ziyarta, abinda ya sa ba a sanin abin da ke kaiwa yana komowa.

Kuma Jamhuriyyar Nijar na daya daga cikin irin wadannan kasashe. Kasa ce da jama'arta ba su waye sosai ba.

A kasar da ke fama da Sahara da kuma dazuka, yawancin jama'a na zaune ne tare da dabbobin da suke kiwo da kuma ayyukan karfi.

Wani rahoto da 'yan Najeriya suka wallafa a baya, ya nuna cewa kashi takwas cikin dari na 'yan kasar ta Nijar na yin ayyukan bauta.

Abin kunya

A watan Fabrerun shekara ta 2005, wata tawagar BBC da ta ziyarci Nijar, domin ganewa idanunsu ko gaskiya ne akwai bayi a kasar, ta ci karo da wata mata mai suna Fatima, wacce ke da 'ya'ya bakwai.

Fatima ta gayawa tawagar BBC cewa ba za ta iya tuna lokacin da ta fara yiwa mai gidanta aiki ba.

Ta ce mai mai gidan nata ba ya biyanta, sai dai yana ba ta abinci sannan ya dinka mata kaya.

"Ta ce bani da kudi, don haka yaya zan yi? "ina bukatar abinci, ga ni da yara, idan akalla zan samu wanda zai ba ni abinci to da sauki."

Ta ji kunya sosai lokacin da wakiliyar BBC ta tambaye ta ko ita baiwa ce? amma bayan ta sunkuyar da kanta sai ta amsa.

Image caption Wasu daga cikin rumfunan da bayi ke zaune a Nijar a shekara ta 2005

Dimaucewa

Amma lokacin da BBC ta tattauna da mai gidan Fatima, sai ya musanta cewa tana bauta. An haramta bauta a Nijar a shekara ta 2003.

An dai haramta cinikin bayi a kasar tun lokacin mulkin mallakar Turawan Faransa, amma ba a fito fili an haramta mallakar bayin ba.

Yawancin bayin dai wadanda aka kama ne lokacin yaki shekaru da dama da suka wuce. Tawagar ta BBC ta ce ta dimauce kan abinda ta gani.

Assibit, wata baiwa ce da ta tsere daga hannun mai gidanta, inda ta bar mijinta wanda shi ma bawa ne.

Image caption A shekara ta 2005 ne a haramta bauta a hukumance a Nijar

Lokacin da tawagar BBC ta nemi bin diddgin inda mijin nata yake, sai wanda ke mallakarsa ya hana shi yin magana da su, sannan 'ya'yan shi suka dinga yi mu su barazana, abinda ya tilas ta mu su ficewa daga yankin.

A baya dai kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun ta kiraye-kirayen da a kawar da bauta a kasar, abinda mahukunta suka ce babu ita a kasar ko kadan.

A shekara ta 2005, an so a gudanar da wani biki a birnin Tahoua inda aka shirya 'yanta bayi fiye da 500, amma gwamnatin kasar ta hana.

Ita dai gwamnatin kasar ta ce tana iya kokarinta domin hana wannan dabi'a wacce a kasashen yamma ake yiwa kallon rashin wayewa.