Shugabar WFP ta kai ziyara Nijar

Josette Sheeran
Image caption Josette Sheeran

Shugabar hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya, WFP ko PAM, ta soma ziyarar kwanaki biyu a jamhuriyar Niger.

Mrs Josette Sheeran ta je kasar ne, domin ganin halin da miliyoyin jama'a ke ciki, sakamakon karancin cimaka.

Tun farko a yau hukumar samar da abincin ta nemi karin gudunmawar kudade, domin taimakawa kimanin mutane miliyan takwas a Niger din, wadanda ba su da isashiyar cimaka.

Haka nan kuma hukumar ta yi alkawarin ribanya taimakon da ta ke baiwa jamhuriyar Nijar.

Mutane kamar miliyan takwas ne aka yi kiyasin suna fuskantar matsalar karanci abinci a kasar ta Nijar.