Za a rantsar da kwamishinonin hukumar zaben Najeriya

Taswirar Najeriya
Image caption A yau za a rantsar da kwamishinonin hukumar zaben Najeriya

A ranar talata ne ake saran shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya,farfesa Attahitu Jega zai rantsar da sababbin kwamishinonin hukumar na wasu jihohin kasar.

Za a gudanar da bikin rantsawar ne a hedikwatar hukumar zaben dake Abuja.

A lokacin da yake rantsuwar daukar aikin,Shugaban hukumar ya ce sahihin zabe a kasar zai tabbata ne kawai idan aka samu shugabannin hukumar masu riko da gaskiya.

Wannan dai wani muhimmin mataki ne a shugabancin hukumar, musamman ganin yadda lokacin zaben shekarar 2011 ke kara matsowa.

Najeriya na fama da matsalar magudin zabe,abinda ya yi sanadiyar koma-bayanta.