Juyin mulki da kalubalen siyasa a Nijar

A lokacin da Nijar ta samu 'yancin kai daga Turawan Faransa, shugaban farko da majalisar kasar ta zaba shi ne Diori Hamani, wanda ya yi mulki tsakanin shekarar 1960 zuwa da 1974.

A tsakanin 1968 da 1973, kasar Nijar ta yi fama da wani wani matsanancin fari, wanda ya yi sanadiyyar asarar kayan amfanin gona, abin da kuma ya jefa kasar cikin matsanancin karancin abinci.

A shekarar 1974, sojoji sun hambarar da gwamnatin shugaba Diori Hamani, bayan da suka zargi gwamnatin da cin hanci da rashawa, hadi ga matsalar fari da ta dabaibaye kasar.

Daga shekarar 1974, Laftanal Kanal Seyni Kountche ya shugabanci gwamnatin mulkin sojan Nijar na tsawon shekaru goma sha uku, inda Allah ya yi ma sa rasuwa a shekarar 1987, bayan ya yi fama da sankarar kwakwalwa.

Bayan rasuwar Seyni Kountche, Hafsan hafsoshin kasar Kanal Ali Seybou ya gaje shi, bayan hawansa mulki a shekarar ya sauya kundin tsarin mulkin kasar a shekarar 1989, wanda ya kai Nijar Jamhuriya ta biyu mai tsarin jam'iyya daya tilo.

Kuma Kanal Ali Seybou ya ajiye kaki ya tsaya takarar shugaban kasa, wanda aka sake zabarsa a matsayin shugaban farar hula a jamhuriyar ta biyu.

Image caption Douda Malam Wanke ya shugabanci Nijar ta hanyar juyin mulki a shekarar 1999

Dage takunkumin adawa

Kungiyoyin kwadago da dalibai sun yi ta kiran da a baiwa jam'iyyun adawa damar shiga a dama da su a harkokin siyasar kasar.

Matsin lambar ta sa a shekarar 1990, shugaba Seybou ya dage takunkumin hana jam'iyyun adawa a kasar.

Har ila yau a shekarar 1990 ne kuma, al'ummar Abzunawa suka fara bore a yankin Arewacin kasar.

Wannan ya sa an kafa sabbin jam'iyyun adawa da kungiyoyin farar hula da dama, abinda ya sa aka kaddamar da wani babban taron kasa wato Conference Nationale a watan Yulin shekarar 1991.

Babban taron ya samar da sabon kundin tsarin mulkin da ya ba shugaba Ali Seybou mukamin jeka -na- yi- ka, aka kuma nada Andre Salifou a matsayin shugaban rikon kwarya na kasar har zuwa lokacin da aka gudanar da zabe.

Majalisa ta sa hannu kan sabon kudin tsarin mulkin kasar wanda ya kai Nijar Jamhuriya ta uku a shekarar 1992.

A shekarar 1993, an gudanar da zabe inda Mahamane Ousman ya lashe zaben shugaban kasa karkashin tutar jam'iyyar CDS Nasara, wadda ta lashe kujeru masu rinjaye a majalisar dokokin kasar.

A shekarar 1995, an kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnati da 'yan tawayen Abzinawa wadanda ke bore a Arewacin kasar.

Image caption Tandja Mamadou ya shugabanci Nijar bayan ya lashe zaben shekarar 1999

Karin juyin mulki

A shekarar 1996, Kanal Ibrahim Bare Mainasara, ya jagoranci kifar da gwamnatin Mahamane Ousman, bayan da aka samu rikici tsakanin shugaban kasa da Fira minista a shekarar 1995, kan zaben majalisar dokokin da aka gudanar.

A watan Mayu na 1996, Kanal Bare ya nada wani kwamiti da zai sauya kundin tsarin mulkin kasar, wanda aka amince da shi bayan kada kuri'ar jin ra'ayin jama'a, abinda ya kai kasar ga jamhuriya ta hudu.

A watan Yuli na 1996, Kanal Bare ya lashe zaben shugaban kasar da ya shirya, abinda ya ba shi damar ci gaba da kasancewa shugaban kasa, har zuwa watan Aprilun shekarar 1999.

A ranar 9 na watan Aprilun shekara ta 1999 ne, aka kashe Kanal Bare a wani juyin mulki da masu tsaron lafiyarsa suka aiwatar, inda Manjo Daouda Malam Wanke ya karbi shugabancin kasar.

Image caption Saliou Djibou ya hau mulki sakamakon juyin mulkin watan Fabrerun shekara ta 2010

Bayan hawansa mulki a wannan shekarar, Manjo Dauda Malam Wanke ya kafa wani kwamiti da zai sa ido kan rubuta sabon kundin tsarin mulkin dake da yanayin tsarin mulkin Faransa da na shugaba mai cikakken iko.

Kuma a watan Agusta na shekarar ne aka amince da sabon tsarin mulkin a wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka kada.

A watannin Oktoba da Nuwamba na 1999, an gudanar da zaben da masu sa ido na ciki da wajen kasar suka ce an yi shi cikin gaskiya da adalci, kuma jam'iyyar MNSD ce ta lashe zaben, wanda ya dora Mamadou Tandja kan karagar mulki.

A shekara ta 2002, sojoji suka yi bore a gabashin kasar da kuma babban birnin Yamai, domin neman a biyasu albashinsu da kuma kyautata rayuwarsu.

Tun a wannan lokacin shugaba Tandja ke jan ragamar Nijar har zuwa ranar 18 ga watan Fabrairun shekara ta dubu biyu da goma inda sojoji suka hambarar da gwamnatinsa, kuma a halin yanzu Janar Salou Djibo ke shugabancin kasar.