Sharhi kan tarihin Jamhuriyar Nijar

Jama'ar Nijar
Image caption Wasu 'yan Nijar ke nan suna kokarin dibar ruwa a wata rijiya a garin Gadabeji

Adadin jama'a

Kidayar jama'ar da aka gudanar a shekara ta 2009 a Nijar, ta nuna cewa yawan jama'ar kasar ya haura miliyan goma sha biyar.

Kidayar ta kuma nuwa cewa kashi tamanin da daya cikin dari na jama'ar kasar na zaune a yankunan karkara ne. Duk da arzikin albarkatun kasar da Allah ya yiwa Nijar, kimanin kashi sittin da biyar cikin dari na jama'ar kasar na rayuwa kan kasa da dalar Amurka daya, kwatankwacin kudin CFA 530 a rana (Watch Fluctuation na canji dala).

Batun cin hanci da rashawa da ake zargin shugabannin kasar na yi na taka rawar gani a halin talaucin da kasar Nijar ke ci gaba da fuskanta.

Image caption Nijar na daga cikin kasashe mafiya talauci a duniya

Fannin ilimi

A Jumhuriyar Nijar, tilas ne a ba kowanne yaro mace ko namiji mai shekaru shidda ilimin Firamare. Sai dai kuma yaran da ake sawa a makarantun Firamaren ba su da yawa musaman ma dai 'ya 'ya mata. kimanin kashi sittin cikin dari na yaran da suke kammala aji shida a Firamare maza ne, inda a yawancin lokuta ake tura yaran aiki a maimakon zuwa makaranta, musamman a lokutan damina.

Haka kuma akwai yaran makiyaya wadanda ba su da takamaiman matsuguni, ballantana makarantu.

Fannin Lafiya

Bangaren kiwon lafiya na da matukar rauni a jamhuriyar Nijar, dalilin da ya sa kasar take kan gaba cikin jerin kasashen da aka fi samun yawan mutuwar kananan yara a kasashen da ke makwabtaka da ita, musamman sabili da rashin ingantaccen abinci mai gina jiki da yaran ba sa samu.

A cewar kungiyar kare kananan yara ta Save the Children, Nijar ita ta fi kowace kasa a duniya yawan mace- macen kananan yara.

Har ila yau kasar na fama da yawan mutuwar mata masu juna biyu lokacin haihuwa.

Zirga zirga

Batun zirga- zirga na da muhimmancin gaske ga tattalin arzikin Nijar, inda hamada da manyan tsaunuka suka rarraba yankunan kasar musamman ta Arewaci.

Tun asali, babbar hanyar zirga- zirga a Nijar ita ce ta rakuma da wasu dabbobi ko bisashe kuma a wasu wuraren kamar kudanci da yammaci a kan yi amfani da 'yan abubuwan da ake da su ta ruwa da ba su da yawa.

Image caption Rashin kyawawan hanyoyi da sahara ya sa jama'a da dama amfani da dabbobi wajen zirga zirga

Kuma hakan bai sauya ba ko lokacin mulkin Turawa. Har yanzu dai babu hanyar dogo ko jirgin kasa kuma ko kwalta babu a titunan da ake da su a lokacin mulkin Turawa.

Bayan da kasar ta samu 'yancin kai, sannu a hankali an samu manyan tituna da ake yawan zirga -zirga ta kananan motoci ko tasi, safa safa da manyan motocin daukar kaya.

Babban filin jirgin saman kasar shi ne na Diori Hammani dake a birnin Niamey. Akwai kuma wasu manyan filayen jirgin saman a Agadez da Zinder.