Boren Abzunawa a Nijar

Boren Abzunawa a Nijar
Image caption Abzunawa sun dade suna nuna damuwa kan yadda al'amura ke tafiya a kasar

Karancin ruwan saman da aka yi a Niger a shekarar 1985 ya haifar da wani mummunan fari wanda ya yi matukar kamari a Arewacin kasar, yankin da yawanci Abzinawa makiyaya ke zaune.

A wannan shekarar Abzinawan dake zaune a Libya sun kafa wata kungiya mai suna Popular Front for the Liberation of Niger (FPLN).

Abzinawan na zargin gwamnatin Nijar da yin halin ko in kula da yankinsu, lamarin da ya sa 'yan kungiyar su ka kai hari a jahar Tchintabaraden, wanda ya kai ga rufe kan iyakokin Nijar da Libya da Algeria, aka kuma tada dubban Abzinawa da makiyayan dake wajen.

Yayin da gwamnatin Ali Seybou ta gaza cika alkawarin tallafin da ta yiwa Abzinawan da suka dawo daga Algeria, sai wasu Abzinawa suka kai hari kan wani ofishin 'yan sanda a Tchintabaraden a watan Mayun shekarar 1990, lamarin da ya kai ga mutuwar mutane 31, kuma 25 daga cikinsu 'yan tawaye ne.

Tun da farko dai babban abinda 'yan tawayen suke nema shi ne na ba 'yayansu damar koyan harshen Abzinawa na Tamashek a makarantu, sai dai kuma nan da nan abin ya rikide ya koma na neman 'yancin cin gashin kai.

'Yan tawayen Abzinawa karkashin kungiyar FLAA da FLT sun ci gaba da gwagarmaya a Arewacin kasar musamman yankin Agadez, inda 'yan yawon bude ido ke zuwa da kuma garin Arlit inda ake hakar ma'adanin Uranium.

Image caption A shekara ta 2005 ne gwamnati ta cimma yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan tawayen

A shekarar 1994, manyan kungiyoyin 'yan tawaye biyu da ake da su a Niger sun amince su ajiye makamai. Kuma a shekarar 1995, duka bagarorin suka sa hannu kan ajiye makamai a birnin Ouagadougou na Burkina Faso.

Rashin cika alkawarin da gwamnati ta yi na daukar tsaffin 'yan ta wayen aikin soji da kuma tallafawa sauran ya sa 'yan tawayen hangen komawa 'yar gidan jiya.

An yi ta cece kuce game da kama ministan yawan bude ido Rhissa ag Boula a shekara ta 2004, bisa zarginsa da hannu a kisan wani dan siyasa a yankin Agadez, Adam Amanghe, amma an yi masa afuwa bayan shekara guda.

A farkon shekara ta 2007, 'yan tawayen karkashin kungiyar MNJ sun ci gaba da kai hari a yankin Arewacin Nijar inda har gwamnati ta kafa dokar takaita zirga-zirga a yankin.

Har sai a watan Aprilun shekara ta 2009 ne a wajen wata ganawa da suka yi a Tripoli babban birnin kasar Libya, gwamnati ta cimma 'yarjejeniyar tsagaita wuta da 'yan tawayen.

A watan Agustan shekara ta 2007- Gwamnati ta baiwa sojojin kasar damar tunkarar 'yan tawayen.

A watan Disamban shekara ta 2007, aka kama wasu 'yan jaridar Faransa guda biyu, da ke aiki da wani gidan talabijin na Jamus, bayan da suka yi hira da 'yan tawayen Abzunawan.