Shugaban Sudan ya je Chadi duk da sammacin kama shi

Shugaban Sudan Omar al-Bashir
Image caption Shugaban Sudan Omar al-Bashir

Shugaban Sudan, Omar al-Bashir, ya isa kasar Chadi domin halartar wani taron kolin shugabannin yankin, duk da cewa kotun duniya mai shari'ar mugayen laifufuka, ta bada sammaci har sau biyu naa kama shi.

Wani minista a gwamnatin kasar Chadin ya ce ba za su kama shugaba al-Bashir ba.

Wannan shine karon farko da shugaban na Sudan ya je wata kasar da ke da wakilci a kotun duniyar, tun bayan da kotun ta tuhume shi da keta hakkin bil'adama da kuma aikata kisan kare dangi a yankin Darfur.