Daraktar WFP ta ziyarci wasu kauyuka a Nijar

Ms Josette Sheeran
Image caption Ms Josette Sheeran

Babbar daraktar hukumar samar da abinci ta duniya, WFP ko PAM, Mrs Josette Sheeran na ci gaba da wata ziyara a jamhuriyar Nijar.

A lokacin ziyarar, Ms Josette Sheeran ta ziyarci garuruwan Dai-Beri da Koriya-Hausa wadanda ke cikin jihar Tillabery a yammacin kasar.

Mutane da dama ne suka yi dandanzo a wurin rarraba kayan abinci da Mrs Josette Sheeran ta ziyarta.

A lokacin ziyarar ta kara kira ga kasashen duniya da su bayar da taimakon gaggawa ga mutane miliyan takwas da matsalar yunwa ta shafa a kasar ta Nijar.

Wasu jami'an gwamnatin Nijar da suka take mata baya a lokacin ziyarar, wadanda suka hada da Kanar Abdulkarim Goukoye, sun ce har yanzu akwai bukatar a tallafawa Nijar a wanann gwagwarmaya da take da matsalar karancin abinci.