Za a raba tsohon minista da mukamin SAN

Taswirar Najeriya
Image caption Mai yiwuwa jama’ar Najeriya sun fara wayewa wajen yaki da matsalar rashawa da kuma rashin shugabanci na gari

A Najeriya, mai yiwuwa tsohon ministan shari'ar kasar, Cif Michael Aondoakaa ya rasa mukaminsa na babban lauya, wato Senior Advocate of Nigeria (SAN) a Turance.

Hakan dai ya biyo bayan koken da wata kungiya mai zaman kanta wadda ake kira Commitee for the Defence of Human Rights ta shigar a gaban hukomomin kasar, inda ta nemi a haramtawa Mista Aondoakaa amfani da mukamin babban lauya a kasar.

Ita dai kungiyar ta Committee for the Defence of Human Rights ta shigar da kuka ne a gaban Shugaban kasa Goodluck Jonathan da kuma Ministan Shari’a Muhammad Adoke, inda ta ke zarginsa da nuna wadansu dabi’u da suka sabawa dokokin aikin lauya a kasar, da yin sama-da-fadi da kudaden gwamnati a lokacin da ya rike mukamin minista.

Shi dai Mista Aondoakaa ya sha fuskantar zarge-zarge tun bayan da ya sauka daga mukamin na minista bayan rasuwar Marigayi Shugaba Umaru Musa ’Yar’aduwa.

Daya daga cikin zarge-zargen dai shi ne irin rawar da ya taka wajen kin amincewa da tasa keyar tsohon gwamnan Jihar Delta, James ibori, zuwa kasar Burtaniya, inda ake zarginsa da halalta kudin haram.

Sai dai kuma ba wannan kadai ne kalubalen da Mista Aondoakaa ke fuskanta ba, domin kuwa wata babbar kotu a kasar ta haramtawa tsohon ministan sake rike wani mukami na gwamnati bisa zargin cewa ya ki gurafanar da kansa a gaban kuliya duk da sammacin da kotun ta aike masa.

Sai dai wani na hannun daman Mista Aondoakaa ya shaidawa BBC cewa tsohon ministan ya daukaka kara a kan wannan batu da hujjar cewa ba a yi masa adalci ba.

Wani kalubalaen da Mista Aondoakaa ke fuskanta kuma shi ne haramcin shiga Amurka da gwamnatin kasar ta yi masa.

Wani jami’in ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya tabbatarwa BBC da hakan, ko da yake ya ce ba zai fadi dalilin da ya sa suka dauki wannan mataki ba.

Idan har kukan da kungiyar ta shigar ya yi nasara, to hakan zai kasance karo na farko da za a haramtawa wani wanda ya rike mukamin minista amfani da mikamin SAN; kuma mai yiwuwa hakan wata alama ce da ke nuni da wayewar jama’ar kasar da kuma kungiyoyi wajen yaki da matsalar rashawa da kuma rashin shugabanci na gari.