An gano bam da aka dana a birnin Jos.

Jami'an tsaro a birnin Jos, na jihar Plateau.
Image caption Birnin Jos, inda aka gano bam da aka dana.

A Najeriya, yau hukumar 'yan sandan jihar Plateau ta ce ta gano wani bam da aka dana a cikin wani gida da ke yankin Nassarawa Gwom, a karamar hukumar Jos ta Arewa. 'Yansandan sun samu nasarar kwance bam din kafin ya kai ga tashi.

Sai dai sun ce da a ce ya tashi da ya haddasa barna mai yawan gaske.

Jihar Pilato dai ta kwashe wani tsawon lokaci tana fama da rikice rikicen da ake dangantawa da addini da kabilanci.

Rikice rikicen da suka yi sanadiyar salwantar rayuka da dinbin dukiya.