Hukuncin Kotun Duniya kan makomar Kosovo

Tutar Kosovo
Image caption Yankin Kosovo ya yi shelar 'yantar da kansa daga Serbia.

A yau Alhamis ne ake sa ran kotun kasa-kasa za ta yanke hukunci a kan ko shelar samun 'yanci daga Serbia da yankin Kosovo ya yi a shekarar 2008 ya halalta.

Kosovo dai wani yanki ne da ba shi da girma—inda Albaniyawa masu rinjaye da Serbiyawa marasa rinjaye ke zaune—to amma shi ne yankin da aka fi takaddama a kansa a nahiyar Turai.

A shekarun 1990, yankin ya yi fama da daya daga cikin yakukuwan da suka fi kazanta a yankin Balkan lokacin da Serbia ta yi yunkurin murkushe Albaniyawa masu tayar da kayar baya.

Shekaru tara bayan nan ne kuma yankin na Kosovo ya yi shelar 'yantar da kansa daga Serbia.

Sai dai Serbian ta ce ba za ta amince da 'yancin na yankin Kosovo ba, don haka ta nemi jin ra'ayin kotun kasa-da-kasa ta Majalisar Dinkin Duniya.

Hukuncin da kotun za ta yanke dai ka iya yin tasiri a kan ko wanne bangare.

Idan Serbia ta yi nasara, za ta matsa lamba a kan a bude sabuwar tattaunawa a kan matsayin Kosovo a Majalisar Dinkin Duniya.

Idan kuma akasin haka ya faru, za a samu karin kasashe da za su amince da 'yancin kan na Kosovo—tuni dai kasashe sittin da tara suka amince da yankin a matsayin kasa mai cin gahsin kanta.

Kasashen da ke fuskantar kalubale daga yankunan da ke son ballewa, kama daga Spaniya zuwa China, za su zuba ido su ga ko hukuncin kotun zai zama abin koyi a shari'ance, duk kuwa da cewa ba tilas ne a aiwatar da shi ba.