Kotun duniya ta yanke hukunci akan ballewar Kosovo

Yankin Kosovo
Image caption Yankin Kosovo

Kotun kasashen duniya da ke birnin Hague, ta yanke hukuncin cewar shelar samun 'yan cin kan da yankin Kosovo yayi daga Serbia bai keta wata doka ta kasashen duniya ba.

Alkalan kotun guda goma ne suka amince da wannan hukunci yayin da hudu suka nuna rashin amincewarsu.

Wannan hukunci dai na iya yin tasiri ga kungiyoyi masu ra'ayin ballewa a sassa daban daban na duniya.

Ko da ya ke babu wani wajibci na amfani da hukunci, to amma ana jin zai iya kara sabunta yunkurin da Kosovo ke yi na samun kasashen duniya su amince da ita.