Kotun duniya ta ce shelar yancin kan Kosovo bai karya doka ba

Kotun Duniya a Hague
Image caption Kotun Duniya a Hague

Babbar kotun duniya da ke Hague ta yanke hukuncin cewa, shelar samun 'yancin kan da yankin Kosovo yayi daga Serbia, ba ta keta dokokin kasashe ba.

Alkalai goma ne suka amince da hakan, yayin da hudu suka nuna adawa.

Alkali Hiashi Owada, wanda ya bayyana hukuncin, ya ce, kotun ta zartas cewa, shelar samun 'yancin kan, ta ranar goma sha bakwai ga watan Fabrairun dubu biyu da takwas, ba ta sabawa dokokin kasashe ba.

Wannan hukuncin dai ka iya yin tasiri a irin gwagwarmayar da 'yan-aware ke yi a sassa dabam dabam na duniya.

Ba dole a yi aiki da hukuncin ba, to amma ana sa ran Kosovon za ta fake da shi, wajen kare neman amincewar kasashen duniya.

Yawancin kasashen yamma dai sun amince da 'yancin kan Kosovon.

To amma Serbia da kawarta Rasha na adawa da hakan.

Shugaban Serbia, Boris Tadic, ya ce kasarsa ba za ta taba amincewa da abinda ya kira: shelar samun 'yancin kai ta gaba-gadi da yankin Kosovo yayi.

Ya ce nan da 'yan kwanaki masu zuwa, gwamnatinsa za ta yi nazari sosai akan lamarin.

Amirka ta ce ta goyi bayan hukuncin kotun duniyar, yayin da Rasha ta ce tana nan kan bakanta na kin goyon bayan 'yancin Kosovo.