Hukumar zabe ta nemi gyara a dokar zabe

Farfesa Attahiru Jega
Image caption Shugaban hukumar zabe a Nigeria

Hukumar zabe mai zaman kanta a Nigeria ta ce ta shgia tsaka mai yiwuwa a sakamakon gyare gyaren da aka yiwa kudin tsarin mulkin kasar da dokokin zabe.

A bisa gyara-gyaran da majalissun dokokin Nigeria suka amince da su, zaa gudanar da zaben kasa baki daya ne a watan Janairu na shekara mai zuwa.

Hukumar ta ce ya zama wajibi ta nemi majalisun dokoki su yi gyara akan sabbin dokokin zaben.

Daya daga cikin dokokin da hukumar ta yi magana akai itace ta dokar da ta wajabta kammala rajistar masu kada kuru'a watanni ukku gabanin a gudanar da zabe.

Hukumar ta nemi da a gyara wannan doka yadda lokacin kammala rajistar da gudanar da zabe ba zai wuce tsawon wata guda ba.