Gwamnonin Jihohin arewa sun yi taro kan muhalli a Katsina

Matsalar sarar itatuwa
Image caption Matsalar sarar itatuwa

An yi wani taron koli na gwamnonin arewacin kasar a Katsina kan batutuwan da suka shafi kwararowar Hamada da matsalolin da suka dabaibaye muhalli a jihohin yankin.

Taron ya hada wakilai daga ma'aikatun ruwa da muhalli da ayyukan gona na jihohin arewacin kasar .

Wannan taro na da nufin samo sahihan hanyoyin maganin kwararowar Hamada da abinda ke haddasa karancin ruwa a yankunan don samun habakar noma da yaki da talauci.

Matsalar gurgusowar hamada dai matsala ce dake addabar galibin jihobhin yankin arewacin Najeriyar.