Nijar da Burkina sun nemi kotun duniya ta shiga tsakaninsu

Nijar
Image caption Nijar

Kasashen Burkina Faso da jamhuriyar Nijar sun bukaci kotun duniya dake birnin Hague ta shiga tsakaninsu dangane da wata rigimar kan iyaka.

Kashen biyu dai sun dade suna tafka muhawara akan wannan takaddama da taki ci, ta ki cinyewa.

Dukkan kasashen biyu dai Faransa ce ta yi musu mulkin mallaka, kuma a bara ne suka amince su kai wannan batu gaban kotun duniyar.

Tuni kuma kotun ta duniya tace, za ta gano inda ya kamata a shata iyaka tsakanin kasashen biyu a wurin dake da tsayin kilomita kusan dari uku da saba'in da biyar.

Kasashen sun amince akan cewar zasu yi na'am da duk wani hukunci da babbar kotun duniyar za ta yanke akan wannan al'amari.

Bugu da kari kuma sun ce a yayin da ake yin wannan shari'a zasu tabbatar da kwanciyar hankali da zaman lafiya a yankin da suke takkaddama akai ba tare da yin kutse ba.