'Tattalin arzikin Amurka na tangal-tangal'

Shugaban Babban Bankin Amurka, Ben Bernanke
Image caption Kalaman Mista Bernanke sun jawo faduwar darajar hannayen jari a kasuwannin hada-hadar kudade

Shugaban Babban Bankin Amurka, Ben Bernanke, ya ce tattalin arzikin kasar na cikin halin rashin tabbas din ba a saba ganin irinsa ba.

Mista Bernanke ya kuma ce mai yiwuwa sai an sake daukar matakan tallafawa tattalin arzikin idan ya ci gaba da tangal-tangal.

Sai dai shugaban babban bankin na Amurka ya ce yana fatan tattalin arzikin na Amurka zai habaka daidai gwargwado.

Wadannan kalaman na Mista Bernanke dai, wadanda ya yi su a gaban wani kwamitin majalisar dokoki ta Amurka a Washington, sun jawo faduwar darajar hannayen jari a kasuwannin hada-hadar kudade na kasar ta Amurka.

Mista Bernanke ya kuma ce wajibi ne a samu daidaito tasakanin kudaden da gwamnati ke kashewa don habaka farfadowar tattalin arzikin kasar da kuma wagegen gibin kasafin kudin da ke barazana ga ci gaban tattalin arzikin a nan gaba.

“Wagegen gibin kasafin kudin na da muhimmanci domin yana kawo daidaito a harkokin cinikayya da kuma hada-hadar kudade; saboda haka ba zan so a yi gaggawar janye wannan tallafi nan kusa ba.

“A lokaci guda kuma, yana da muhimmanci a samar da wani kwakkwaran shiri na cike gibin a shekaru kadan masu zuwa don a karawa masu zuba jari kwarin gwiwa”, inji Mista Bernanke.

Mista Bernanke ya kuma nuna jin dadinsa da yadda kasashen Turai ke daukar irin matakan da Amurka ta dauka kusan shekara guda da ta gabata don karfafa nasu tattalin arzikin.

A ranar Juma'a ne dai ake sa ran Tarayyar Turai za ta fitar da sakamakon wasu gwaje-gwaje da ta yi don gano ko bankunan Turai za su iya jurewa matsin tattalin arziki nan gaba.