Wasu na adawa da sabon tsarin zabe

shugaban hukumar zabe ta kasa, INEC
Image caption Shugaban hukumar zabe ta Nijeriya, Farfesa Attahiru Jega.

A Nijeriya, wasu jam'iyyun adawa sun fara korafi kan sauyin da aka samu cewa za a fara gudanar da zaben shugaban kasa, da na 'yan majalisar dokoki ta kasa, kafin a gudanar da na gwamnoni da 'yan majalisar dokokin jihohi.

Majalisar dattawa ta Nijeriya ce ta amince da wannan sabon tsari na zabe, a shirye shiryen da ake na zaben shekara ta 2011.

Su dai masu adawa da shirin suna cewa, da zarar an kammala zaben shugaban kasar, za a share fagen magudin zabe kenan.

Daya daga cikin masu wannan korafi shi ne Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa, shugaban jam'iyyar PRP na kasa a Nijeriya.