A Nijar an kori wani jami'i kan rajista

Janar Salou Jibo, shugaban mulkin sojin Nijar
Image caption Janar Salou Jibo, shugaban mulkin sojin Nijar

A jamhuriyar Nijar hadin gwiwar jam'iyyun siyasa na bangaren AFDR da ma 'yan CFDR sun ce sun gamsu da matakin da shugaban mulkin sojan kasar, Janar Salu Jibo, ya dauka na tsige shugaban karamar hukumar Torodi, Manjo Umaru Garba mai ritaya.

A shekaranjiya ne dai jam'iyyun na bangaren AFDR suka shaida ma manema labarai cewa sun gano wani wuri da ake yin katuna da takardun haihuwa na jabu a cikin wani gidan shan barasa a birnin Yamai.

Sun yi zargin yunkurin na yin magudi ne ga zabe na tafe a kasar.

Kungiyoyin biyu sun yi kira ga gwamnatin ta gudanar da bincike mai zurfi domin gano dukkan masu hannu a al'amarin.