Guguwa ta tsayar da aikin toshe rijiyar man BP

Jiragen ruwan da ke aikin toshe rijiyar da ke tsiyayar da mai
Image caption Hukumomin Amurka sun umurci jiragen ruwan da ke aiki a inda mai ya tsiyaya a Tekun Mexico su bar yankin saboda tasowar ruwa da iska mai karfin gaske

Hukumomi a Amurka sun umurci jiragen ruwan da ke aiki a inda mai ya tsiyaya a Tekun Mexico su bar yankin saboda tasowar ruwa da iska mai karfin gaske.

Cibiyar Nazarin Guguwa mai Karfi ta Amurka ta bayyana cewa ruwan da iska mai karfi, wadanda suka taso daga tsibirin Bahamas, za su isa yankin da ake aikin dakatar da tsiyayar man ranar Asabar.

Babban jami'in Amurka mai kula da aikin dakatar da tsiyayar man, Admiral Thad Allen, ya ce umurnin kauracewa yankin zai kawo jinkiri a yunkurin da ake yi na toshe rijiyar man da ke tsiyaya, to amma hukumomi sun fi damuwa ne da kiyaye lafiyar mutanen da ke aiki a wurin.

Kadan ya rage ma'aikatan su kammala aikin da zai kai ga like rijiyar da ke tsiyaya kwata-kwata.

Kauracewa wurin kuma na nufin ba za a sa ido a kan rijiyar man ba har na tsawon kwanaki.

Sai dai Admiral Allen ya ce ko ma dai menene ya faru, marufin da aka sanya a bakin rijiyar, wanda ya yi nasarar dakatar da tsiyayar man na kusan mako guda, ba zai motsa ba.

Ya kuma ce ya umurci kamfanin BP ya tabbatar cewa jami'an da ke sa ido a kan marufin ne za su bar yankin a karshe, sannan kuma su ne farkon komawa bayan ruwa da iskar sun wuce.

Jami'ai sun ce kauracewar za ta jawo jinkirin kwanaki goma zuwa sha hudu a aikin toshe rijiyar man.