Ma'aikatan PHCN na bazanar yajin aiki.

Turakun hukumar wutar lantarki ta Nijeriya.
Image caption Nijeriya ta dade tana fama da karancin wutar lantarki.

Bisa dukkan alamu, Nigeria tana fuskantar fadawa cikin duhu daga ranar Litinin mai zuwa.

Dalilin hakan shi ne yajin aikin da kungiyar ma'aikatan Kamfanin wutar lantarki na kasar ke shirin farawa daga Litinin din.

Ya kuma biyo bayan ikirarin da suka yi ne, cewa gwamnatin tarayya ba ta cika musu alkawarin biyan kudaden ariyas ba.

Sai dai shugabannin kamfanin wutar lantarkin sun bayyana cewa suna iya bakin kokarinsu wajen ganin cewa kungiyar ma'aikatan bata fara yajin aikin ba.

Barazanar yajin aikin ta zo ne a lokacin da ake fama da tsananin karancin wutar lantarkin a Najeriya.