Tattalin arziki da noma a Nijar

Noma da kiwo a Nijar
Image caption Tattalin arzikin jamhuriyar Nijar ya dogara ne kan noma da kiwo

Duk da cewa hamada ta mamaye kusan yawancin jamhuriyar Nijar, kuma bangaren da ba hamadar na yawan fuskantar barazanar fari da gurgusowar hamada, amma yawancin tattalin arzikin Nijar ya ta'allaka ne kan albarkatun noman da ake samu a kudancin kasar inda ake da kasar noma mai kyau.

Sai kuma kiwon dabbobi ko bisashe, wadanda ake fitarwa zuwa wasu kasashe musamman masu makwabtaka da Nijar din.

Karfen Uranium na daga cikin albarkatun kasar da Nijar ke da su wanda shi ma ake fitarwa zuwa kasashen waje.

Sai dai kuma yawan farin da ake samu da kuma matsalar kwararowar Hamada, da karuwar jama'a da ake samu da ma rashin kasuwar karfen Uranium a duniya sun sa tattalin arzikin Nijar na yin kasa.

Image caption A kwanakin nan an samu dan yan mai a Jamhuriyar Nijar

Noma

Na duke tsohon ciniki, noma shi ne babbar sana'ar da jama'ar kasar Nijar suka dogara da ita shekaru aru aru kafin zuwan Turawa, wadda ta hanyar sa ne ake ciyar da kasa kuma ake samun kudin shiga.

Yawanci a kudancin kasar ne kamar Zinder da Maradi da sauran yankuna aka fi yin noma saboda kasar noman da suke da ita. Sai dai kuma a wuraren da ake samun karancin ruwan sama akan yi noman rani.

Jamhuriyar Nijar kan yi fama da karancin ruwan sama, wanda a shekarun 1960 kasar ta fuskancin matsanancin fari, wanda ya haifar da matsalar yunwa da mutuwar dabbobi ko bisashe da dama a kasar.

A watan Agustan shekara ta 2008, gwamnatin Nijar ta bada kwangilar gina madatsar ruwa ta Kandaji a jihar Tillaberi da zummar bunkasa noman rani.

Baya ga noma, kiwon dabbobi ko bisashe na daga cikin hanyoyin da tattalin arzikin Nijar ya ta'allaka a kai, inda ake safarar bisashe kamar rakuma da shanu da raguna da dai sauransu zuwa kasashen waje.