Kungiyar Taliban ta ce ta sake dabara

Jirgin Amurka mai sarrafa kansa
Image caption Abu ne mai wahala a iya tantance tasirin hare-haren jirage masu sarrafa kansu

Reshen Pakistan na kungiyar Taliban ya tabbatar da cewa harin da jiragen saman Amurka masu sarrafa kansu ke kaiwa a yankunan kabilu na Pakistan da ke kan iyaka da Afghanistan yana yin cikas ga ayyukanta.

Tantance irin tasirin da hare-haren jirage masu sarrafa kansu ke yi a yankin kabilun na Pakistan dai na da wahala kasancewar ba a bari 'yan jarida su sake.

To amma an yi amanna cewa su kan yi kafar ungulu ga ayyukan tayar da kayar baya, su rikirkita hanyoyin sadarwa na 'yan Taliban, da kuma tilastawa shugabnnin kungiyar buya.

Sai dai reshen na Pakistan na kungiyar Taliban ya tabbatarwa BBC cewa ya kirkiro wadansu dabaru na kaucewa hare-haren.

A yanzu dai ’ya’yan kungiyar ba sa haduwa a wuri guda, kuma shugabanninsu sun daina amfani da wayoyin salula, sannan kuma ba sa daukar lokaci mai tsawo a wuri guda.

Wani jam'in Taliban a arewacin Waziristan ya shaidawa BBC cewa asarar da jirage masu sarrafa kansu ke jawowa kungiyar ta dan wani lokaci ce kuma a karshe su ne za su yi nasara.

Kungiyar ta ce Amurka ta fi kai hari ne Waziristan; hakan kuma ya sa sauran yankunan kabilun ba su da hadari ga 'yan kungiyar.