Zimbabwe za ta binciki jami'an tsaro

Daya daga cikin wuraren hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba a Zimbabwe
Image caption Ana zargin dakarun tsaro a wuraren hakar ma'adinai da cin hanci da rashawa

Wani minista a gwamnatin Zimbabwe ya shaidawa BBC cewa zai binciki zargin aikata cin hanci da rashawa da ake yiwa dakarun tsaron gwamnati da ke aiki a wuraren hakar ma'adinai na kasar.

Ministan, Savior Kasukuwere, ya fadi hakan ne yayin da yake mayar da martani ga zargin cewa jami'an gwamnatin da ke da alhakin hana hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba suna hada baki da 'yan kasashen waje kuma suna karbar cin hanci da rashawa daga masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba.

Ministan ya kuma kara da cewa yana fatan ganin talakawan kasar ta Zimbabwe sun amfana da arzikin ma'adinan kasar.

A makon da ya gabata ne kasar ta Zimbabwe ta cimma wata yarjejeniya wadda ta ba ta damar fitar da madinanta na lu’ulu’u don sayarwa a kasashen waje.