Sarkin Bauchi Alhaji Suleimanu Adamu ya rasu

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

Allah ya yiwa mai martaba sarkin Bauchi, Alhaji Suleimanu Adamu rasuwa.

Wazirin Bauchin, Alhaji Muhammadu Bello Kirfi ya shaidawa BBC cewa, marigayin ya rasu ne a daren jiya, a wani asibiti da ke birnin Alkahira na Masar, da misalin karfe 12 agogon Najeriya.

Ya ce, a gobe Lahadi ne ake sa ran za a mayar da gawar mamacin gida Najeriya.

Majalisar masarautar Bauchin na zaman tattaunawa kan shirye-shiryen jana'izar sarkin.