Mutane 15 sun rasu a Faretin Soyaya a Jamus

Faretin Soyaya
Image caption Faretin Soyaya

A Jamus akalla mutane 15 sun hallaka, bayan da aka tattake su a lokacin wani bikin kade-kade da raye-raye da ake wa lakabi da Faretin Soyaya - watau Love Parade. Wasu mutanen kimanin 100 kuma sun jikkata.

Lamarin ya faru ne a kofar shiga wurin da ake bikin a birnin Duisburg. Fiye da mutane miliyan guda ne ke halartar Faretin Soyayar.

Duk da mace-macen da aka samu, hukumomi sun yanke shawarar kyalewa a cigaba da sabgar, don gudun kada a sami wani tashin hankalin.

A bara an soke Faretin Soyayar a Bochum, saboda an ga cewa wurin ba zai iya daukar dimbin jama'ar da ake sa ran za su halarta ba.