Nijar na neman kafa tashar nukiliya domin samun lantarki

Shugaban mulkin sojan Nijar Janar Salou Djibo
Image caption Shugaban mulkin sojan Nijar Janar Salou Djibo

Jamhuriyar Nijar na samun wakilci a hukumar makamashi ta duniya, IAEA, kuma tana son samun izinin kafa tashar makamashin nukiliya a kasar, domin samun wutar lantarki.

Praministan Nijar din ne, Dr Mahammadou Dandah ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya kira yau a birnin Yamai, bayan dawowar sa daga taron kolin shugabannin kasashe da na gwamnatoci mambobin kungiyar CEN-SAD, wanda aka kammala jiya a N'Djamena, babban birnin kasar Chadi.

Praministan ya ce sun gabatar da wannan shawara a lokacin taron na CEN-SAD, kuma sun sami goyon baya.

Nijar ce kasa ta biyu a duniya wajen samar da karfen uranium.