Rahotanni sun ce 'yan taliban sun sace sojan Amurka 2

Mayakan Taliban
Image caption Mayakan Taliban

Rahotanni sun nuna cewar mayakan Taliban sun sace wasu sojojin Amurka biyu dake aiki karkashin rundunar dakarun kawance ta ISAF a Afghanistan.

An yi imanin cewa an cafke su ne a lardin Logar, bayan musayar wuta.

Wakilin BBC ya ce, rundunar sojin Amurka ta bukaci a sako mutanen biyu, har ma ta yi tayin ba da lada, ta rediyon yankin.

Sai dai akwai rahotannin da ba a tabbatar ba dake cewa an kashe daya daga cikin sojojin.

Kafin haka dai Amurka ta bada sanarwar an kashe ma ta soja 5 a Afghanistan din, sakamakon wasu hare hare.

A yanzu an kashe dakarun kawance 70 kenan cikin wannan wata a Afghanistan, adadin da shi ne mafi girma cikin wata guda, tun mamayar da aka yi shekaru 9 da suka wuce.