Dakarun NATO na cigaba da neman Amurkawa biyu

Dakarun NATO a Afghanistan
Image caption Dakarun kawancen kungiyar NATO a Afghanistan sun tsinci motar amurkawan nan biyu da aka sace

Dakarun kawance na NATO a Afghanistan dake neman Amurkawa guda biyu wadanda mayakan Taliban suka kama, sun tsinci motarsu.

An yi imanin cewa mutanen wadanda dakarun sojin ruwan Amurka ne, an kama su ne a yankin Logar, bayan musayar wutar da aka yi.

ISAF ta bayyana cewa mutanen sun bace ne, bayanda suka bar gidan da suke zama a Kabul babban birnin kasar.

An shafe dare ana kokarin gano su kuma mahukuntan Amurka sun yi alkawarin bada lada ga duk wanda ya taimaka aka dawo da su, to amma jami'an yankin sun ce daya daga cikin mutane ya rasu.