Atisayen sojin Amurka a yankin Koriya

Jirgin ruwan yakin Amurka
Image caption Jirgin ruwan yakin Amurka a yankin ruwan Korea.

Amurka da Korea ta Kudu sun fara wani atisaye da jiragen ruwan yaki a kusa da mashigin ruwan Korea, a matsayin wani matakin nuna karfin da suke da shi ga Korea ta Arewa, bayan nutsar da wani jirgin ruwan yakin Korea ta Kudun cikin watan Maris.

Jiragen ruwan yaki ashirin, da kuma na sama guda dari biyu ne ke wannan atisaye.

Wani bincike na kasashen duniya da aka gudanar ya gano cewar wani makami mai linzami da aka harba daga jirgin ruwan yakin Korea ta Arewa mai tafiya karkashin teku shi ne yayi sanadiyar nutsar da jirgin yakin na Korea ta Kudu.

Ita dai Korea ta Arewa ta sha musanta zargin, ta kuma sha alwashin daukar fansa kan duk wanda ya kai ma ta hari.