Shugaban kamfanin man BP na shirin barin mukamin

Shugaban BP Tony Hayward
Image caption Shguaban BP Tony Hayward

BBC ta samu labarin cewa shugaban kampanin mai na BP, Tony Hayward, wanda ya sha suka a Amurka sakamakon malalar mai a tekun Mexico, zai sauka daga mukaminsa.

Wata majiya a kampanin BP din ce ta shaida wa wani editan BBC, Robert Peston hakan.

Wata sanarwa da hukumar kampanin ta BP ta fitar a matsayin martani kan batun ta bayyana cewar, Mr Hayward na da cikakken goyon bayan hukumar gudanarwar kampanin.

An kiyasta cewar kampanin na BP zai kashe kimanin dala biliyan 30 wajen gyara barnar da malalar man ta haddasa.