An yi jana'izar mai martaba sarkin Bauchi

Jahar Bauchi a taswirar Najeriya
Image caption Jahar Bauchi a Taswirar Najeriya

An yi jana`izar marigayi mai martaba sarkin Bauchi, Alhaji Suleman Adamu, bayan isar gawarsa Bauchin daga kasar Masar.

A shekaranjiya Juma'a ce Sarkin ya rasu a wani asibiti da ke birnin Alkahira.

Tuni dai gwamnatin jihar Bauchin ta umurci al`ummar jihar dasu yi zaman makoki na sati guda.

Mataimakin shugaban Najeriya, Architect Namadi Sambo, ya na daga cikin manyan jami'an da suka halarci jana'izar sarkin.

Yanzu hankali zai koma ga majalisar sarkin, domin jin wadanda za su yi takarar sarautar.