Likitocin Nijeriya sun janye yajin aiki

Taswirar Nijeriya
Image caption Taswirar Nijeriya, inda likitoci suka janye yajin aiki.

A Nijeriya, kungiyar likitocin dake zurfafa karatu a asibitocin koyarwa na kasa ta dakatar da yajin aikin da likicin suka shafe makonni hudu suna gudanarwa.

Dakatar da yajin aikin ya biyo bayan fara cika wasu daga cikin bukatun da kungiyar ta nema daga gwamnatin tarayya.

Bukatun sun hada da karin albashi, da ware wasu kudade da suka shafi karatun likitocin.

Kungiyar Likitocin ta cwe dakatar da yajin aikin na tsawon makonni biyui ne, domin ta ga kamun ludayin gwamnatin. Ta yi barazanar komawa yajion aikin, idan ta fahimci, babu wani ci gaba a kokarin biya masu bukatun.