Mutane 10 sun hallaka a hadarin tankar mai a Najeriya

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya, fiye da mutane 10 ne suka mutu, ya yin da wasu da dama suka samu munanan raunuka, bayan da wata tankar mai ta fadi a kasuwar Madalla dake kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Wasu da hadarin ya faru a idonsu sun bayyana cewa, tankar ta fadi ne akan wasu motoci dake tafiya akan hanyar, inda daga bisani ta kama da wuta, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar mutanen, tare da kone wasu bangarori na kasuwar.

Lamarin konewar tankar mai na neman zama ruwan dare a Najeriya.

Ko a kwanakin baya wasu mutane sun hallaka a garin Gombe sakamakon faduwar tankar mai.