Rundunar AU za ta kaddamar da farmaki kan yan ta'adda a Somaliya

Rundunar sojojin kasar Uganda, ta bayyana cewar rundunar kiyaye zaman lafiya ta kasashen kungiyar Africa da ke Somalia, ba ta da wani zabi illa ta kaddamar da farmaki gadan-gadan a kan masu kishin Islamar da ke tayar da kayar baya a kasar ta Somalia.

Kakakin rundunar sojojin ta Uganda, Felix Kulayi-gye ya shaidawa BBC, cewar wannan shi ne kawai zabin da ya rage bayan mummunan harin bomb din da masu kiishin Islamar na Somalia suka kai a cikin wannan watan a kasar Uganda.

Yace kamar yadda ka sani ne, an shiga hali ne na gaba kura baya sayaki, don haka ina za ka dosa? Shin za ka zauna ne aka zubawa sauratar Allah ido,za ka bari AlQaeda ta ci gajiyar karfin da suke da shi? Ko kuwa za ka tattara baki dayan nahiyar ce ta tashi haikan domin ta ce, ba za ta amince da taaddanci ba?