Babban jami'in kamfanin man BP zai sauka daga mukaminsa

Babban jami'in kamfanin man BP, Tony Hayward
Image caption Babban jami'in kamfanin man BP, Tony Hayward zai sauka daga kan mukaminsa ran daya ga watan oktoba

Katafaren kamfanin mai na BP ya bada sanarwar cewar babban jami'in kamfanin, Tony Hayward zai sauka daga kan mukaminsa ran daya ga watan oktoba.

Mr. Hayward ya fuskanci suka sosai game da yadda ya tunkari bala'in malalewar mai cikin gabar tekun mexico daga rijiyar man kamfanin data fashe

kamfanin BP ya kuma sanar da cewar Bob Dudley wanda yanzu haka yake rike da mukamin manajan daraktan kamfanin zai maye gurbin Mr. Hayward a matsayin babban jami'in kamfanin.

Kamfanin ya kuma ce yayi asarar dala biliyan goma sha bakwai daga watan Afrilu zuwa watan Yuni bayan aukuwar wannan al'amari

Kamfanin ya kara da cewar zai saida kadarorinsa da kudinsu suka tasamma dala biliyan talatin nan da wasu watanni goma sha takwas masu zuwa