Za'a tura karin dakaru zuwa kasar Somalia

Taswirar kasar Somalia
Image caption Za'a tura karin dakaru zuwa kasar Somalia

Ministan tsaron kasar Somalia Abubakar Abdi Osman, ya ce yana da kwarin gwiwar cewar kasashen Afirka za su aike da karin dakaru zuwa Somalia, domin karfafa aikin kiyaye zaman lafiya na tarayyar Afirka wato AMISOM.

A wata hira da yayi da BBC, Mr. Abdi ya ce yana goyon bayan a sake dorawa dakarun na AMISOM aikin daukar matakan soji don murkushe mayakan Al Shabaab.

Tuni dai ministan yada labaru na Somaliyan Abdirahman Omar Yarisow ya sabunta kiraye kirayensa, na karawa dakarun kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa karfi, ciki har da kasashen musulmi.

Batun rikicin kasar Somaliyan na daga cikin batutuwa da aka baiwa mahimmanci sosai a taron shugabannin kasashen Afirka