Iran na fuskantar matsin lamba

Kasar Iran
Image caption Kasar Iran na cigaba da fuskantar matsin lamba daga kasashen turai saboda shirinta na nukiliya

Iran na cigaba da fuskantar matsin lamba kan shirin nukliyarta a yayinda ministocin hulda da kasashen wajen tarayyar turai ke daukar matakai masu karfi akan kasar.

Matakan dai sun hada da takunkumi kan abun da ya shafi zuba jari a sashin mai da kuma iskar kasar.

Sauran sun hada da sashin kudin kasar da kuma jami'an juyin juya halin kasar.

Jami'an kasar Iran din dai sun amince da cewar yawan gangunan man da kasar ke hakowa sun ragu da dubu dari biyu da hamsin a kowacce rana

Tuni dai shugaban kasar Mahmood Ahmedinajad ya maida martani inda yayi amfani da lafazi mai zafi.