Gwamnonin arewacin Najeriya za su yi taro a Kaduna

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Image caption Gwamnonin arewacin Najeriya za su yi taro yau a Kaduna kuma ana sa ran batun tsarin nan na karba karba na jam'iyyar PDP na daga cikin mahimman abubuwan da zasu tattauna

A yau ne ake sa ran gwamnonin arewacin Najeriya za su yi wani taro a jahar kaduna dake arewacin kasar.

Cikin abubuwan da ake sa ran za su tattauna sun hada da batun nan na tsarin karba- karba da jam'iyyar PDP ta amince da shi wajen fitar da 'yan takarar mukamai, musamman ma na shugaban kasa.

Ana ganin gwamnonin zasu maida hankali akan wannan batu ne ganin yadda batun ke ci gaba da haifar da baraka tsakankanin 'yan jam'iyyar.

A halinda ake ciki dai, tsarin jam'iyyar dake mulkin kasar wato PDP, shine, yanzu lokaci ne na Arewacin kasar ta fidda dan takara, to amma wasu sun gwammace shugaban kasar mai ci Dr. Goodluck Jonathan ya tsaya takarar, duk da cewa daga yankin kudancin kasar ya fito.

Wannan batu dai na cigaba da haifar da kace na kace a arewacin kasar, tsakanin masu kaunar tsarin da masu son ganin an soke shi don shugaba Goodluck Jonathan ya tsaya takara