Al'ka'ida ta kashe Michel Germaneau

Shugaban kasar Faransa Nicholas Sarkozy ya tabbatar da cewa dan kasar Faransar da aka yi garkuwa da shi Michel Germaneau, an kashe shi a hannun wani reshe na Alqaeda a Arewacin Afrika.

Shugaba Sarkozy yayi kira ga 'yan kasar da su guji yin tafiya zuwa yankin Sahel musamman bangaren da dake da iyaka da kasashen Chadi, da Mali, da Mauritania, da Niger.

Shi dai Mr Germaneau ma'aikacin agaji ne wanda aka sace a watan Afrilu lokacin yana aiki a wata makaranta.

Mr Sarkozy ya kira wani taro na mayan jami'an tsaro a kasar domin tattaunawa kan irin martanin da za a mayar.