Tarrayar Afrika za ta kara dakaru zuwa Somalia

Tarrayar Afrika za ta kara dakaru zuwa Somalia
Image caption Somalia na fuskantar rikicin shugabanci musamman daga kungiyoyin addini

Taron kolin kungiyar kasashen Afrika (AU) a Uganda ya amince da kara tura sojojin kiyaye zaman lafiya dubu biyu zuwa Somalia, domin maganin hare haren da kungiyar Al-Shabaab ke kaiwa a can.

Wannan karin zai kai yawan sojojin kungiyar AU'n zuwa dubu takwas kenan. Duk da ya ke shugaban Uganda, Yoweri Museveni ya nemi a karfafa aikin rundunar yadda sojojinta za su iya shiga yaki, to amma a karshe kungiyar ba ta sauya aikin rundunar ba.

Shugaban na Uganda ya nemi kasashen duniya dasu kai dauki domin daukar dawaniyar kungiyar.

An dai kashe daruruwan mutane ne a makwanni biyu da su ka gabata a wani hari da kungiyar Al-shabab ta ce ta kai a Kampala babban birnin Uganda.

Wannan harin dai ya tunzura Shugaba Yoweri Museveni inda ya bukaci kungiyar AU da murkushe kungiyar Al-shabab.

Masana na ganin matakin kara sojoji da kungiyar ta yi ba zai yi tasiri ba, amma zai taka rawar gani wajen tabbatarda da canji a shugabancin kasar.

Harwa yau dai masana na ganin cewar karin sojojin a Somalia zai haddasa karin mutuwar mutane a kasar, saboda kungiyar Al-shabab za ta ci gaba da kai hare hare.

Wakilin BBC a Gabashin Afrika Will Rose, ya ce akwai yiwuwar cewa karin sojojin da za samu a yanki za su fito ne daga kasar Guinea da Djibouti, amma har yanzu dai babu wani takamaiman lokacin da za a tura sojojin.

Kafin taron kasashen Afrika da aka yi a Kampala , gwamnatin Somalia ta nemi tarrayar Afrika da ta tura dakaru daga kasashen musulmi domin rage tunzura kungiyar Al-shabab.

Kasashen Guinea da kuma Djibouti dai suna da Musulmai masu rinjaye, amma babu tabbas ko kungiyar ta Al-shabab za ta amince da dakarun da za su fito daga kasashen.