Kamfanin BP ya yi alkawarin gyara kurakurai

Bob Dudley
Image caption Sabon shugaban yana da jan aiki a gaba

Mutumin da aka shirya shine zai zama babban Jami'in gudanarwa na kamfanin Man nan na BP, ya bayyana cewa wani karamin Kamfani mai cike da hikimar aiki ne zai bayyana, bayan rikicin da ake fama da shi wanda ya shafi barna da Mai yayi a yankin tekun Mexico.

Bob Dudley, wani ba-Amurke, wanda a yanzu shi ne manajan dirakta na kamfanin na BP, ya shaidawa wani gidan talbijin na Amurka, cewar abun da zai fi baiwa fifiko shine aikin da ake yi gyara wuraren da man yayi barna.

Ya ce, "Abu na farko a kan jerin abubwan da zan sa gaba shi ne in tabbatar mun dode rijiyar, kuma yin hakan, ya kawo karshen malalar da mai yake yi daga ciki, sannan mu tsaftace dukkanin bakin tekun, mu maido shi yadda ya ke a da. Wanann kuma abu ne da za mu dade muna yi."