Sabon Shugaban Kamfanin mai na BP ya ce Kamfanin zai kasance karami mai kuma hikima

Bob Dudley
Image caption Bob Dudley, Sabon Shugaban Kamfanin mai na BP

Mutumin da aka shirya shine zai zama babban Jami'in gudanarwa na kamfanin man nan na BP, ya bayyana cewa wani karamin Kamfani mai cike da hikimar aiki ne zai bayyana, bayan rikicin da ake fama da shi wanda ya shafi barna da Mai yayi a yankin tekun Mexico.

Bob Dudley, wani ba-Amurke, wanda a yanzu shine manajan dirakta na kamfanin na BP, ya shaidawa wani gidan talbijin na Amurka, cewar abun da zai fi baiwa fifiko shine aikin da ake yi gyara wuraren da man yayi barna.

Ya ce abu na farko a kan jerin abubwan da zai sa gaba shi ne,ya tabbatar da cewar sun dode rijiyar, kuma yin hakan, ya kawo karshen bulbular da mai ke yi daga ciki, sannan su tsaftace dukkanin bakin tekun, su kuma maida shi yadda ya ke a da.

Ya ce wanann kuma abu ne da zasu dade suna yi.