Gwamnonin arewa sun ce kowa na iya takara

Shugaba Goodluck Jonathan
Image caption Ko wane mataki shugaba Goodluck zai dauka?

Gwamnonin arewacin Najeriya wadanda suka gudanar da wani taro a Kaduna a yau sun yanke hukunci dangane da batun nan na karba karba ko kuma, batun da ke haifar da ka-ce-na-ce a kan ko wane ne zai tsaya wa jam'iyyar PDP takara a shekara ta 2011.

A karshen wannan taro dai gwamnonin sun yanke hukuncin cewa shugaban kasar, Goodluck Jonathan, kamar kowane dan Nijeriya, zai iya tsayawa takara.

Haka kuma jam'iyyar PDP, wadda ta zayyana karba-karba a kundin tsarin mulkinta, tana da hurumin komawa ta duba wannan tsari nata.