Nazari kan takunkumin da aka sanyawa Iran

Tashar nukiliyar Iran
Image caption Tashar nukiliyar Iran, wacce take jawo kace nace a duniya

Iran dai na cigaba da fuskantar matsin lamba kan shirin nukliyar ta bayan da kasashen duniya suka kara sanya mata takunkumi.

Na baya bayan nan shi ne matakan da ministocin harkokin waje na Tarayyar Turai suka dauka, wadanda suka hada da takunkumi kan abun da ya shafi zuba jari a sashin mai da kuma iskar gas din kasar.

Sauran matakan za su hada da sashin kudi da kuma jami'an tsaron juyin juya halin kasar.

Tuni dai shugban Ahmedinajad ya maida martani inda yayi amfani da lafazai masu zafi.

Wakilin BBC a Iran Jon Leyne, wanda yanzu haka yake birnin Alkahira, ya ce masa'anatar hada sinadarin mai a Assaluyeh ta kasance batun da aka fi baiwa fifiko wajen hada shirye shirye masu kayatarwa wadanda ake nunawa a gidan talibin din gwamnatin kasar.

Wani jami'in gwamnatin kasar ya ce a shekaru goma da suka gabata an kammala gina goma daga ciki masana'antun hada sinadarin mai, kuma biyar daga cikinsu sun fara aiki a shekaru biyu da suka gabata. Hakan ya sa yawan man da kasar samarwa ya karu da kashi hamsin cikin dari.

Image caption Yadda harkokin kasuwanci ke tafiya a kasar Iran, ko wannan takunkumin zai yi tasiri kan kasar?

Dangantaka da Najeriya

Yayin da kasar Iran ke ci gaba da fuskantar matsin lamba na wannan takunkumin, a Najeriya wasu 'yan kasuwa da masana al'amuran kasa da kasa na ci gaba da tsokaci dangane da halin da harkokin kasuwancin tsakanin kasashen biyu ke ciki.

Yayin da wasu masana ke cewa takunkumin ba zai yi wani tasiri ba ga harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

Wasu 'yan kasuwa a Najeriyar kuwa na cewa, mai yiwuwa takunkumi yayi tasiri a harkar dangantaka tsakanin gwamnatocin kasashen biyu.

Huldar kasuwanci

Najeriya da kasar Iran dai sun dade da kulla dangantaka tsakaninsu ta fuskoki daban daban, inda bincike ya nuna cewa 'yan Najeriyar da dama ne baya ga harkokin kasuwanci kanje 'kasar ta Iran domin karatu.

Ko a 'yan kwanakin nan ma sai da kasar Iran din ta yi alkawarin musayar fasahar makashin nukiliya tsakaninta da Najeriya.

Image caption Kasashen duniya dai na fatan ganin matakin ya sanya kasar sauya tunani kan shirin nukiliyarta

Sai dai kasancewar takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai suka kakabawa kasar kan shirinta na nukiliya, ko wani hali harkokin kasuwanci dake gudana tsakanin Najeriya da kasar ta Iran ke ciki?

Alhaji Ali Abbas Usman Jega na daya daga cikin 'yan kasuwar Najeriya dake gudanar da harkokin kasuwanci da 'yan kasuwa a kasar Iran.

Kuma ya ce baya ganin takunkumin zai yi wani tasiri kan harkokin kasuwancin da ke tsakanin kasar da kasashe irinsu Najeriya.

Sanya takunkumi ga wata kasa a duniya dai wani mataki ne da za'a iya cewa ba samun abu bane a dangartaka tsakanin kasashen duniya.

Kokarin da BBC ta yi na jin tabakin jakadan kasar Iran a Najeriya kan adadin yawan kasuwancin dake gudana tsakanin Najeriya da Iran din dai ya ci tura, domin jakadan kasar yace ba zai yi magana dangane da wannan batu.

Irin hali na tsaka mai wuya da kasar ta Iran ta tsinci kanta a ciki sakamakon takunkumin da aka kakaba mata yasa tuni wasu masana ke cewa mai yiwuwa kasar ta ci gaba da kasancewa saniyar ware a duniya muddin aka kasa cimma masalaha dangane da takaddamar shirinta na nukiliya.