Ingiza Biritaniya aka yi cikin yakin Iraki

Hans Blix
Image caption Da karfi da yaji aka ja Biritaniya

Babban Sufetan duba makamai na Majalissar Dinkin Duniya gabanin a fara rikicin kasar Iraqi, Hans Blix, ya bayyana cewa an ja kasar Britaniya ne shiga yakin da sam babu wata doka da za ta goyin bayansa.

Mr Blix yana magana ne da BBC bayan da ya bayyana a gaban wani kwamitin bincike a kan yakin Iraki a nan London. inda ya bayyana shakkarsa a kan hikimar Shugaba Bush da Priyi minista Tony Blair ta yanke shawara kaddamar da wannan yaki a daidai lokacin da ake tabka muhawarar dacewa ko rashin dacewar yakin.

Ya ce, "Ina ganin, darasi shi ne an ja Birrtania ne cikin yakin da bai kamata sam sam ta shiga ba, sannan kuma yaki ne da ba za a iya karewa a gaban shari'a ba.

Kana Birttania ta fi mutunta ka'idojin Majalisar Dinkin Duniya fiye da Amurka.