Gwamnonin arewacin Najeriya na yin taro a Kaduna

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Image caption Gwamnonin arewacin Najeriya za su yi taro yau a Kaduna kuma ana sa ran batun tsarin nan na karba karba na jam'iyyar PDP na daga cikin mahimman abubuwan da zasu tattauna

Gwamnonin Arewacin Nijeriya na gudanar da wani taro a Kaduna, inda ake sa ran zasu tattauna kan batun karba-karba a zaben shekara ta 2011.

Ana ganin gwamnonin za su maida hankali a kan wannan batu ne ganin yadda batun ke ci gaba da haifar da baraka tsakankanin 'yan jam'iyyar.

A halin da ake ciki dai, tsarin jam'iyyar dake mulkin kasar wato PDP, shi ne, yanzu lokaci ne na Arewacin kasar ta fidda dan takara, to amma wasu sun gwammace shugaban kasar mai ci Dr. Goodluck Jonathan ya tsaya takarar, duk da cewa daga yankin kudancin kasar ya fito.

Wannan batu dai na cigaba da haifar da kace na kace a arewacin kasar, tsakanin masu kaunar tsarin da masu son ganin an soke shi don shugaba Goodluck Jonathan ya tsaya takara

Batun na karba-karba dai na daga cikin batutuwan dake jan hankali sosai a Nijeriya musamman ma a jam'iyyar PDP.

A jiya dai gwamnonin jam'iyyar ta PDP a kudu maso kudancin Nijeriya sun amince da su goyawa shugaba Goodluck Jonathan baya a zabe mai zuwa, yayin da ake sa ran gwamnonin arewacin kasar suma za su fitar da na su matsayin a yau.