Koma baya game da shige da fice a jahar Arizona

Zanga zanga game da shige da fice a Arizona
Image caption Zanga zanga game da shige da fice a Arizona

Alkalin wata kotun tarayya a Amurka ya hana aiwatar da wani bangare na wasu sabbin tsauraran dokoki da suka shafi shige da fice, wadanda gwamnatin jihar Arizona ta amince da su, aka kuma shirya za a fara amfani da su gobe alhamis.

Kungiyar nan ta Civil Liberties Union, wadda ta kalubalanci dokar, ta gabatar da hujjar cewa wannan sabuwar doka, ta shiga gonar gwamnatin tarayya wajen tantance dokar shige da fice ta kasa.

A cikin watan Afrilu ne 'yan majalisar jihar Arizona suka amince da dokar, a wani yunkuri na rage yawan bakin hauren da ke shiga cikin jihar ba tare da izini ba daga makwabciyar kasar Mexico.

Shugaba Obama ya ce matakin ya saba hankali, yayin da kungiyoyin 'yan latin Amurka suka ce nuna banbancin launin fata ne.